A shirin Mahangar Zamani mun tattauna da matashin ɗan Majalisar Wakilai, Bello El-Rufai kan salon siyasarsa da kuma abin da yake son cimmawa a siyasance.
Bello ya kuma bayyana mana ra’ayinsa game da tsamin dangantakar da ke tsakanin mahaifinsa, tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da gwamnan jihar na yanzu, Uba Sani.